Zaben ′yan majalisa a jihohi uku a Jamus | Labarai | DW | 13.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben 'yan majalisa a jihohi uku a Jamus

An dai zura ido a ga yadda jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel za ta taka rawa a zaben da ke da muhimmanci a siyasar ta Jamus a wannan lokaci.

Deutschland Landtagswahl Sachsen-Anhalt

Wurin kada kuri'a a Sachsen-Anhalt

A ranar Lahadin nan kimanin masu kada kuri'a miliyan 12 ke gudanar da zaben 'yan majalisa a wasu jihohi uku na Jamus wato Baden-Württemberg da Rhineland-Palatinate da ke a Kudu maso Yammaci da Saxony-Anhalt da ke a Gabashi. Zaben da irinsa bai cika daukar hankali ba a lokutan baya, sai dai a wannan karo saboda zura idon al'umma na kasar ta Jamus da ma wasu kasashe na waje, ana dako aga yadda za ta kaya ganin yadda batun 'yan gudun hijira da shugabar gwamnati Angela Markel ta yi ruwa ta yi tsaki a kansa, ya zama shi ne abin da ake duba, wanda kuma shi ake ganin ta yiwu ya sanya jam'iyyar CDU ta Markel din ta sha mamaki. Sai dai wasu na ganin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Da take karkare nata kamfe a ranar Asabar a jihar Baden-Württemberg Merkel ta sha alwashin maida 'yan gudun hijira masu kwarara Jamus saboda dalilai na tattalin arziki gida. Sai dai ta sake jaddada aniyarta ta bada kariya ga 'yan gudun hijira da suka shiga kasar saboda dalilai na neman jinkai.