Zaben Tunisiya na gudana lafiya | Labarai | DW | 26.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Tunisiya na gudana lafiya

Ana cigaba da kada kuri'a a zabukan majalisar dokokin Tunisiya wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Zainul Abideen Ben Ali.

Masu aiko da rahotanni sun ce mutane da dama na kan dogayen layuka inda suke shirin kada kuri'a a sassa daban na Tunis babban birnin kasar.

Firaministan kasar Mehdi Jomaa ya ce zaben na yau abu ne na tarihi inda a hannu guda ya jinjinawa al'ummar kasar dangane da yadda suka yi fitar dango wajen zaben mutanen da za su wakilce su.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu labarin tashin hankali ba ko da dai dama mahukuntan kasar sun ce sun tsaurara matakan tsaro a wuraren zabe wanda takara ta fi zafi tsakanin jam'iyyar Ennahada ta Rachid Ghannouchi da kuma Nidaa Tounes da Beji Caid Essebsi ke jagoranta.