Zaben shugabannin PDP ya bar baya da kura | Siyasa | DW | 11.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben shugabannin PDP ya bar baya da kura

Takaddama ta sake kunno kai a jam'iyyar PDP mai adawa bisa sakamkon zaben shugabanin jamiyyar da ta yi a babban taronta a Abuja, inda wasu ‘yan takarar da suka sha kaye ke nuna ja da cewa an musu ba dai dai ba.

Sakamakon zaben shugabanin jamiyyar da aka gudanar a Abuja ya bar baya da kura saboda korafe-korafe da ma kurari na daukan mataki da wasu yayan jamiyyar ke yi, musamman bangaren da suka sha kaye, kuma suke ganin ba'a rabu da bukar da zargin dauki dora ba a jamiyyar.

Wannan yanayi da ke jefa tsoron ci gaba da fuskantar sarkakiyar a jam'iyyar da ta ke fatan shawo kan matsalolin da suka yi mata dabaibayi. Aliyu Musa Usman Manji  ya nemi takarar zama mataimakin shugaban jamiyyar na yankin arewacin Najeriya yace su kam ba'a yi masu adalci ba.

Tun ana kirga kuru'u ne dai Farfesa Tunde Adeniran da aka fafata das hi, amma duk da tagomashi day a samu na goyon baya daga jiga-jigan jamiyyar irin su tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ma Janar Babangida bai kai labara ba. Abinda ya sanya daraktan yakin neman zabensa Garba Gajam bayyana cewa.

To sai dai ga tshohon gwamnan jihar Jigawa Alh Sule Lamido da ke zama jigo a jamiyyar ta PDP ya ce su wajensu zabe ya yi kyau kuma kamata ya yi a yi murna ga hakan.

A yayin da ake fuskantar masu suka da nuna ‘yar yatsa ga zaben ga sabon mataimakin shugaban jamiyyar ta PDP Sanata Sanata Babayo Garba Gamawa yace sauyin da aka samu alamu ne na samun nasara.

Kwararru na bayyana tsoron abinda ka iya biyo baya daga sakamakon zaben jamiyyar ta PDP da ta ke kokari na dinke barakata, domin shi kansa sabon shugaban Uche Secondus yace suna fad a jan aiki a gabansu.

Sauti da bidiyo akan labarin