Zaben shugaban kasar Mali | Labarai | DW | 28.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasar Mali

Zaben shugaban kasar Mali na gudana lami lafiya a mazabu daban-daban, lamarin da shugaban rikon kwaryar Mali Dioncounda Traore ya yaba da shi bayan kada kuri'arsa.

Shugaban ya ce zaben na wannan karon shi ne mafi kyau a jerin zabukan da kasar ta shirya tun bayan da ta samu 'yancin kanta a shekara ta 1960.

Mr. Traore ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a guda daga cikin rumfunan zaben kasar dubu 21, inda ya kara da cewar ya yi matukar farin ciki da yadda zaben ke gudana musamman ma dai dagane da yadda aka tsara shi.

An dai bude rumfunan zabe ne a kasar da misalin karfe 8 agogon GMT kuma kimanin 'yan kasar kusan miliyan bakwai ne za su kada kuri'unsu domin zaben shuagaban da jagorancesu daga cikin 'yan takara 27 da ke zawarcin kujerar shugaban kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da ake gudanar da zabe a kasar tun bayan da soji su ka hambarar da gwamnatin farar hula cikin shekarar da ta gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe