Zaben shugaban kasa a Saliyo | Labarai | DW | 07.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Saliyo

Masu zabe a kasar Saliyo sun fara kada kuri'a a wannan Laraba don zaben sabon shugaban da zai jagoranci kasar na wani sabon wa'adin, bayan shudewar zamanin shugaba mai ci Ernest Bai Koroma.

Sierra Leone Wahlen 2007 (Getty Images/AFP)

Wata matar da ke kada kuri'arta a wata mazaba dake birnin Freetown

Masu zabe a kasar Saliyo sun shirya don zaben sabon shugaban da zai jagoranci kasar na wani sabon wa'adin, bayan shudewar zamanin shugaba mai ci Ernest Bai Koroma. 'Yan takara 16 ne dai ke fafatawa a zaben ciki har da mata biyu, sai dai ana sa ran takarar ta yi zafi ne tsakanin Samura Kamara na jami'yyar All Peoples Congress mai mulki, da kuma Julius Maada Bio na babbar jam'iyyar adawa ta SLPP.

Wannan ne dai babban zabe na farko da kasar ta Saliyo za ta yi bayan fuskantar annobar cutar Ebola da ta lakume rayukan mutane aklla 4000 a shekara ta 2014. Haka nan ma kasar ta fuskanci Ibtila'in zaizayewar kasa a bara, da nan daruruwan mutane suka salwanta. Akwai dai bukatar dan takara ya sami kashi 55 cikin dari na kuri'un da za a kada, kafin ya kaiga zama shugaban kasa. Mutum miliyan uku ne ake sa ran za su kada kuri'a a zaben.