Zaben shugaban kasa a Kwalambiya | Labarai | DW | 27.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Kwalambiya

Al'ummar kasar Kwalambiya na gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa, karo na farko tun bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen kungiyar FARC.

'Yan takara biyu ne dai ake ganin za su taka rawar gani a wannan zabe zagaye na farko da suka hada da Ivan Duque na jam'iyya mai mulki da ta jima tana mulki a kasar, sai kuma dantakarar bangaran adawa Gustavo Petro wanda tsohon magajin garin Bogota babban birnin kasar ta Kwalambiya ne.

Zaben na ranar Lahadin 27 ga watan Mayu da muke ciki dai, na da matukar mahimmanci ga kasar ta Kwalambiya, wadda ta kama hanyar samun zaman lafiya tun bayan sasantawa da 'yan tawayen FARC da suka shafe sama da shekaru 50 suna tawaye a kasar, kafin daga bisani kungiyar ta rikide ta zama ta siyasa. Ta shafinsa na Twitter shugaban kasar mai barin gado Juan Manuel Santos ya yi kira ga 'yan kasar da su fito su yi dafifi domin kada kuri'unsu.