Zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya | Labarai | DW | 30.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Wannan zabe dai shi ake sa ran zai zamo madubi na irin inda kasar ta sa gabanta ganin kaurin sunanta a rikici mai nasaba da tashin hankali saboda banbancin addini.

Zentralafrikanische Republik Referendum

Jami'i da kayan zabe a Bangui

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira da a gudanar da zabe mai inganci da zai yi sanadi na samun zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Sakataren majalisar ta Dinkin Duniya ya yi wannan kirane a ranar Talata.

Zaben shugaban kasa da na 'yan majlisa da za a yi a wannan kasa a ranar Laraban nan shi ake sa ran zai zamo madubi na irin inda wannan kasa ta sa gabanta, tun bayan shigarta rudani biyo bayan juyin mulki a shekarar 2013.

Mista Ban da yake kira ga duk masu ruwa da tsaki a zaben kasar da su tabbatar da ganin an gudanar da zaben lami lafiya, ya bayyana cewa dakarun Majalisar masu aikin wanzar da zaman lafiya karkashin MINUSCA za su yi aiki tukuru wajen ganin an gudanar da zabe lafiya, sannan ya bukaci duk 'yan siyasar kasar da su bi hanyoyi na zaman lafiya da ma na shari'a dan kalubalantar duk wani mataki da bai musu daidai ba a zaben.

'Yan takara talatin ne dai ke neman kujerar shugabancin wannan kasa sai dai uku na gaba gaba da ke ciki har da dan takara Musulmi da ya taba rike ministan harkokin waje.