Zaben shugaban kasa a Gini Konakry | Siyasa | DW | 06.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben shugaban kasa a Gini Konakry

Masu neman mukamin shugaban kasa a kasar Gini na cigaba da fafutuka wajen zawarci kuri'un jama'a a zaben da za a yi ranar Lahadi.

Masu lura da tafiyar harakokin siyasar kasar ta Gini Konakry na ganin cewa daga cikin 'yan takara bakwai da za su fafata da Shugaba Alfa Conde a zaben da kasar da zai gudanar ranar Lahadi mai zuwa madugun 'yan adawar kasar Cellou Dallein Diallo da kuma Sydia Toure na jam'iyyar UFR ne 'yan takarar da ka iya kasancewa babban kalubale ga shugaban mai ci musamman ganin irin yanda ra'ayinsu ya zo daya wajen neman kawar da shugaba Conde daga kujerarsa.

Guinea Wahlkampf 2015

'Yan siya na cigaba da gangami don neman kuri'un al'umma.

Abubacar Diakite da ke yin sharhi kan lamuran siyasar kasar ta Gini na ganin hakan na yiwuwa a wannan karo amma akwai sabanin ra'ayi a tsakaninsu a kan hanyar da ya kamata su bi domin su cimma wannan buri nasu inda ya ke cewa ''dukkannin 'yan adawa na da burin ganin an samu canjin shugabanci to sai dai suna da sabanin ra'ayi a tsakaninsu"

Sabanin da ke da akwai tsakanin Cellou Dalein Diallo da Sydia Toure dai shi ne na maganar tsayar da dan takara daya a tsakanin 'yan adawa wanda tuni Sydia Toure ya bada shawara, to sai dai Cellou Dalein Diallo ya yi watsi da wannan shawara ta Mr. Toure batun da ya sanya suka kai ga raba gari.

Präsidentschaftswahlen in Guinea-Bissau 2014

Jam'iyyun adawa na fafutuka wajen raba shugaba Alpha Konde da kujerarsa

Masu sharhi kan lamuran siyasar kasar ta Gini dai na ganin rashin hadin kan 'yan adawa a wannan zabe na iya baiwa Shugaba Conde wata babbar garabasa ta samun nasara a zaben ba tare da wani tarnaki ba. Sai dai duk da haka 'yan kasar da dama ne ke ganin a wannan karo 'yan adawar kasar na da babbar sa'a ta lashe zaben.

Wannan zabe dai zai gudana ne a cikin wani hali na zaman dar dar inda a fakon wanann mako mutun daya ya mutu a yayin da wasu kimanin 80 suka ji rauni a sakamakon wata taho mu gama da ta hada magoya bayan jam'iyyun adawa da na masu milki a kasar. Abin da ya kai ga kafa dokar hana yawon dare a wasu unguwannin birnin Konakry.

Sauti da bidiyo akan labarin