1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adama Barrow na neman ta-zarce

Usman Shehu Usman ZMA
December 3, 2021

Al’ummar Gambiya na zaben shugaban kasa a wannan Asabar, zaben da ke zama na farko tun bayan wanda ya jagoranci hambare Yahya Jammeh bayan shekaru 20 na mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/43oZY
Gambia Parlamentswahlen 2017
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ko ba komai dai wasu ‘yan kasar ta Gambiya na ganin cewa, bayan kawar da Mulkin Yahya Jammeh an samu abu mai kama da demokradiyya, inda akalla suke iya tofa albarkacin bakinsu kan lamarin mulkin kasar, wanda zamanin Jammeh babu wannan damar, a cewar mutane kamar Souleymane Mane da ke Banjul babban birnin kasar:

"Na gani a shekaru biyar da suka gabata mun samu demokradiyya a kasarmu. Mutane na da yancin yin Magana”.

Yayin da wasu ‘yan kasar ta Gambiya ke sukar shugaba Adama Barrow da karya alkawuran zabe da ya yi cikin shekaru biyar kan mulki, amma ga wasu ‘yan kasar dai basa boye goyon bayansu ga shugaba Barrow, kamar Binta Fay:

"Adama Barrow na da matukar son mutane. Yana basu damarmaki. Muna son kasancewa tare da Barrow iya rayuwarmu”.

Shi dai Adama Barrow a zaben da ya gabata alkawuransa sun fi karkata ne ga ayyukan raya kasa, kuma a wannan zaben ma ba wani alkawari da yayi illah cewar zai dora daga inda ya tsaya na ayyukan raya kasa, amma a zahirance ko da Banjul babban birnin kasar babu alamu na kwarai kan ayyukan raya kasa da yayi a shekaru biyar da ya yi kan Mulki.