Zaben shugaban kasa a Benin | Labarai | DW | 08.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Benin

Tawagar jami´ai da suka sa ido game da yadda zabe ya gudana a kasar Benin , sun yaba game da yadda zabe na shugaban kasa ya gudana a kasar cikin kwanciyar hankaki da lumana.

Mambobin tawagar da suka fito daga wasu kasashe shida na yammacin kasashen Africa 6, karkashin Mr Patrick Houessou, sun kuma tabbatar da cewa masu zabe sun fito yadda yakamata don kada kuri´´un su a lokacin wannan zabe.

To sai dai kuma jami´an sun koka a game da bacewar katinan zabe sama da miliyan daya, na wadanda suka can can ci yin zabe a kasar.

A dai gobe alhamis ne ake sa ran bayyana sunan mutumin daya lashe wannan zabe a cikin yan takarar shugabancin kasar 26.

Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin yan takarar matukar babu wanda ya samu rinjaye to za a koma zagaye na biyu ne kawai a tsakanin wadanda suka samu rinjaye a lokacin zagaye na farko.