Zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki a Ruwanda | Siyasa | DW | 17.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki a Ruwanda

Al’umar Ruwansa za su gudanar da zaben raba gardama kan gyara kundin tsarin mulki domin Shugaba Paul Kagame ya sake samun damar tsayawa takara a zaben shekara ta 2017 domin yin tazarce

Al’umar kasar Ruwansa za su gudanar da zaben raba gardama bisa gyara kundin tsarin mulki domin Shugaba Paul Kagame ya sake samun madafun iko yayin da wa’adin mulkinsa ke kawo karshe a shekara ta 2017, abin da ke fuskantar suka daga kasashen duniya.

Idan ana ruwan-sama a Ruwanda lamuran rayuwa su kan tsaya cak. Daruruwan mutane suka taru a wata makaranta cikin ruwan a wajen birnin Kigali fadar gwamnatin kasar domin nuna goyon baya yayin gangamin neman gyara ga kundin tsarin mulki. Akwai alluna da aka kafa da ke neman kada kuri'ar amincewa. Mutanen abin da za su zaba ke nan. A wannan Alhamis 'yan Ruwanda mazauna kasashen ketere za su yi zaben, sannan a Jumma’a a yi zaben raba gardama cikin kasar baki daya.

Shugaba Paul Kagame na Ruwanda ya yi wa’adi na biyu na mulki shekaru bakwai-bakwai da kundin tsarin mulki ya tanada, inda wa’adin na shekaru 14 ke kawo karshe a shekara ta 2017, karkashin kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi Kagame ba ya da izinin sake takara.

Wani sashe na 'yan Ruwanda na goyon bayan zaben raba gardamar kasar

Zeno Mutimura ya kasance dan majalisar dokoki daga jam’iyya mai mulki ta Rwanda Patriotic Front (RPF) ga abin da yake cewa a wajen wani gangami:

"Mutane sun tambaya gyara ga kundin tsarin mulki domin shugaban ya sake samun wata dama ta takara a shekara ta 2017."

Kimanin 'yan Ruwanda milyan 3 da dubu 700 suka saka hannu kan takardar da ke neman gyara kundin tsarin mulki wanda aka mika wa majalisar dokoki. Idan aka amince da gyara ga kundin za a sake zaben Shugaba Paul Kagame na tsawon shekaru bakwai, daga nan kuma zai iya sake takara na wa'adin mulki na shekaru biyar sau biyu, wanda ke zama iyaka ga shi da kuma duk wanda zai karbi madafun iko nan gaba. Haka ya nuna Kagame zai shekaru 21 na bakwai sau uku da kuma biyar sau biyu, abin da ke zama shekaru 31 idan aka hada jumla.

Ra'ayin masu adawa da zaben raba gardama a Ruwanda

Masu adawa da tsarin irin Gonza Muganwa na ganin abubuwa da suke faruwa suna dakile demokaradiyya:

"Ba abu ne da ke nuna tsarin siyasa ba. Amma abu mai kyau shi ne sun amsa cewa ba haka ne ya dace ba saboda babu masu adawa."

Kasashen duniya na adawa da shirin tazarcen Shugaba Kagame

Kasashen duniya sun nuna takaici bisa abin da ke faruwa a Ruwanda, inda babbar jami'ar kula da harkokin kasashen ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta ce haka ya zama mulkin mutum daya, wanda ya saba tanadi da ka'idojin demokaradiyya.

Carine Maombi ke zama babbar sakatare ta babbar jam'iyyar adawa ta Democratic Green Party of Rwanda (DGPR) wadda ta ce an hana su wata dama ta wayar da kan mutane:

"Mun je wajen hukumar zabe ta ce babu lokacin da za mu yi yakin neman zabe ko kuma mahawara."

Shugaba Paul Kagame yana da goyon baya bisa ayyukan ci-gaba da ya aiwatar amma har yanzu bai ce komai ba kan yuwuwar zai sake takara.