Zaben raba gardama cikin tashin hankali a ZAR | Siyasa | DW | 14.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben raba gardama cikin tashin hankali a ZAR

'Yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kimanin miliyan biyu sun kada kuri'a a zaben raba gardama na sabon kundin tsarin milkin kasar. Sai dai zaben ya gudana cikin tashin hankali da ya haddasa mutuwar mutane.

.'Yan kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kimanin milkiyan biyu ne suka fito a jiya Lahadi inda suka kada kuri'arsu kan sabon kundin tsarin milkin kasar wacce ta share shekaru uku tana fama da yakin basasa. Matsaloli na rashin samun damar kintsa zaben a cikin lokaci da yanayi na matsalar tsaro da yanzu haka a ke ci gaba da kasancewa a cikinsa a kasar sun taimaka ga samar da latti wajen bude runfunan zaben da soma zaben gadan-gadan. Tashin hankalin ya barke a lokacin zaben a birnin Bangui da sauran biranen kasar, kamar yanda ta kasance a birnin Kaga-Bandoro na Arewa maso Tsakiyar kasar inda mutanen Noureddine Adam, jagoran kungiyar FPRC wani reshe na tsohuwar kungiyar 'yan tawayen Seleka suka cinna wuta tare da lalata illahirin kayayyakin zabe da aka kai a birnin. Irin haka ta kasance a birnin Bossangoa cibiyar tsohon Shugaban kasar Francois Bozize wanda kotun ta cire sunansa daga cikin 'yan takara. Sai dai da yake tsokaci kan wannan batu Gervais Lakosso jagoran kawancan kungiyoyin fararn hula na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cewa ya yi duk wadannan matsaloli bai kamata su sanyaya kaurin 'yan kasar ba shirya zabuka a kasar shi ne hanya mafi a'ala wajen kawo karshen matsalolin da kasar ta tsinci kanta a cikinsu.

Kungiyoyin farar hula na goyan bayan zabukan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

" Muna san cewa 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya lokaci ya yi na su bayyana ra'ayinsu domin rana ta zo ta samun 'yancin fadin albarkacin baki da kuma 'yancin zaben daya daga cikin mutane 30 da suka tsayar da takarar neman shugabancin kasar. Kenan yau rana ce da bai kamata mutun ya bari wasu su turza shi ba. Mun san cewa zai wuya a iya gudanar da zabe a cikin tsanaki, amma dai ya kamata zaben ya zama tsarkakakke"

Suma dai daga nasu bangare kasashen duniya na yin kira na bai wa al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar kwarin guywa tare da bayyana masu aniyarsu ta rakasu a cikin wannan sabuwar tafiya tasu har zuwa gacci. Aurelien Agbenonci mataimakin rundunar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato MUNISCA ya ce duk da barazanar da ake fiskanta sun dauki matakai na ganin ko ta halin kaka wadannan zabuka sun gudana.

Rundunar MUNISCA ta sha alwashin tabbatar da tsaro a lokuttan zabe

"Lalle akwai wasu yankunan inda ke da akwai wasu kungiyoyi masu ikrarin kasancewa gagarau da suke cewa ba za su bari a kai kayan zaben balantana a gudanar da shi ba. To ina mai tabbatar maku cewa za mu shawo kansu domin mu rundunarmu ta zaman lafiya ce ba ta yaki ba, dan haka za mu nemi mu tattuna da su domin yin sulhu da zai ba mu damar kai kayan zaben wadanda akasarinsu an isar da su a gurin zaben"

An koma gudanar da zaben na raba gardama a safiyar wannan litanin a unguwar musulmi ta PK5 inda harin da wasu 'yan bindiga suka kai a unguwar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar a jiya Lahadi ya cilasta dakatar da zaben. Kuma yanzu haka jami'an tsaro na rundunar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dama sojojin Faransa sun ja daga a kewayen unguwar ta PK5 musamman a bakin runfar zabe ta makarantar Baya Dombia inda aka kai harin rokar a ranar Lahadin. Kawo yanzu dai babu wani tashin hankali da ya sake tashi a birnin sannan babu wani da ya fara shigo a game da zaben raba gardamar wanda ke zamowa tamkar wani zakaran gwajin dafin zaben shugaban kasa a jimilce da na 'yan majalissar dokoki da kasar za ta shirya a ranar 27 ga watan Disamba da muke ciki idan Allah ya kaimu.

Sauti da bidiyo akan labarin