Zaben raba gardama a Masar cikin rigingimu | Labarai | DW | 22.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben raba gardama a Masar cikin rigingimu

Al'umar kasar Masar na kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben raba gardama a kan daftarin kundin tsarin mulkin kasar da ake takaddama kansa.

Jam'iyyar 'yan uwa Musulmi da ke mulki a kasar ta yi kira ga 'yan kasa da su kada kuri'ar amincewa da kundin tsarin mulkin da 'yan adawa masu sassaucin ra'ayi suka yi fatali da shi. Ana hasashen amincewa da kundin tsarin mulkin gani yada yan kishin islama ke samun goyon baya a kauyukada kananan biranen fiye da manyan biranen kasar. Sakamakon zagayen farko na zaben da ya gudana a wancan mako ya bayyanar da cewa kashi 57 cikin 100 daga cikin jama'ar wadannan wurare sun kada kuriar amincewa da kudin tsarin mulkin. Mutane sama da 30 suka samu raunuka a kazamar arangamar da aka yi yayin zanga zangar nuna adawa da kundin tsarin mulki da aka yi a ranar Juma'a. An tura sojoji dubu 120 da 'yan sanda kusan dubu 130 domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal