1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya da karancin wutar lantarki a Afirka ta Kudu

Mohammad Nasiru AwalFebruary 13, 2015

Dage zaben Najeriya da matsalar hasken wutar lantarki a Afirka ta Kudu da kuma gasar cin kofin kwallon kafar Afirka na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi tsokaci kai a wannan mako.

https://p.dw.com/p/1EbIB
Nigeria Wahlkommision verschiebt Wahltermin Attahiru Jega
Hoto: Stringer/AFP/Getty Images

A sharhin da ta yi game da dage zaben Najeriya jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi.

An shiga halin rashin tabbas a fagen siyasar Najeriya bayan da hukumar zaben kasar ta dage lokutan gudanar da zaben da makonni shida bisa dalilai na rashin tsaro wanda tun da ma ya tabarbare. Wasu manazarta na kallon wannan matakin da wani juyin mulkin soji. Domin yayin da lokacin zaben ke kara karatowa yana fitowa fili cewa shugaba mai ci Goodluck Jonathan ka iya faduwa a zaben. Jaridar ta ce shugaban wanda ya hau kan karagar mulki kimanin shekaru biyar da suka wuce yanzu ya zama tamkar wani dan jeka na yi ka kuma maras angizo a tsakanin masu rike da madafun iko irinsu janar-janar na soja da attajiran kasar da kuma shugabannin 'yan mafiya.

Ayyukan Boko Haram da siyasar Najeriya

Anschlag in Gombe, NIgeria 02.02.2015
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Ita kuwa a sharhinta jaridar Die Zeit ta fara ne da tambayar shin Boko Haram na barazana ga demokradiyyar Najeriya? Ta ce hukumar zabe ta INEC ta dage zaben bisa hujjar cewa yakin da ake yi da Boko Haram na bukatar sojoji da yawa, saboda haka ba bu tabbas na gudanar da zabukan cikin cikakken yanayi na tsaro. To wai shin wata kungiyar 'yan tarzoma da kiyasi ya nuna tana da mayaka 10000, za ta iya tarwatsa tsarin siyasar wata kasa mai al'umma fiye da miliyan 170? Shin kungiyar tana barazana ga demokardiyyar Najeriya? Ko shakka babu Shugaba Goodluck Jonathan zai ce a'a. Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro ya ce za a murkushe kungiyar cikin makonni shida, amma ayar tambaya ita ce shin mai yasa sai yanzu za a samu nasara cikin makonni shida a kan abin ya gagari magancewa cikin shekaru shida? Abin dai da walakin wai goro a miya.

Matsalar wutar lantarki ga tattalin arziki

Daga batun siyasar Najeriya sai na makamashin wutar lantarki a Afirka ta Kudu, inda labarinta jaridar Die Tageszeitung ta ce Afirka ta Kudu na fuskantar barazanar daukewar wutar lantarki gaba daya.

Symbolbild Stromausfall Südafrika
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Ludbrook

Ta ce tsarin samar da wutar lantarki ya tsufa sannan an samu karuwar yawan masu amfani da wutar. Yanzu haka kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasar wato Eskom yana yawan dauke wuta, abin da ba a saba da gani ba a kasar. Tuni dai wannan matsalar ta yi babbar illa ga tattalin arzikin kasar. Yanzu dai gwamnatin kasar ta dora fatanta a kan tashar samar da makamashi ta Medupi wadda za ta fara aiki a cikin watan Yuni.

Gasar AFCON ta 2015

A ranar Lahadi aka kammala gasar cin kofin kwallon kafar Afirka da kasar Equitorial Guinea ta karbi nauyin shiryawa. A labarinta game da gasar jaridar Der Tagesspiegel cewa ta yi kasar Cote d'Ivoire ta lashe gasar Afrika Cup, amma babbar wadda ta yi asara ita ce hukumar kwallon kafa ta Afirka wato CAF. Jaridar ta ce hargitsin magoya bayan Equatorial Guniea da ya yi sanadin jikkata 'yan Ghana kimanin 30 da rashin iya alkalanci na wasu alkalan wasa da cin tara mai yawa ga wasu kasashen da hukumar CAF ta yi da fargabar barkewar cutar Ebola sun so dakushe armashin gasar ta bana.