1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisun dokokin jihohi uku a Jamus

Kamaluddeen Sani/ MNAMarch 13, 2016

Sakamakon farko na bayan zaben jihohi uku ya nuna cewa jam'iyyar 'yan ra'ayin rikau ta AfD ta taka rawar gani. CDU ta Angela Merkel ta yi asarar kuri'u a jihohi biyu daga cikin uku saboda manufarta ta 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/1ICWK
Deutschland Landtagswahl Rheinland-Pfalz AfD Wahlparty Uwe Junge
Magoya bayan AfD suna murnar nasara a jihar Rhineland-PalatinateHoto: picture alliance/dpa/R. Holschneider

Rahotanni da ke futowa yanzu haka a dangane da sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin jihohi uku da aka gudanar a wannan Lahadi a tarayyar Jamus, na nuni da cewar jam'iyyar shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta sha kasa.

A jihar Saxony-Anhalt da ke gabashin kasar, kamar yadda sakamakon farko na bayan zabe ya nunar, jam'iyyar AfD ta samu kusan kashi 23 cikin 100 wanda haka ya sanya ta jam'iyyaa ta biyu mafi karfi tana biye da jam'yyar CDU wadda ta tashi da kashi 29 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. Ita kuma SPD ta samu kashi 11 cikin 100 biye da jam'iyyar Die Li9nke wadda ta tashi da kashi 17 cikin 100.

Jam'iyyar AfD da ke hammayya da CDU ta Angela Merkel ta samu gagarumin karin kuri'u a zaben wanda hakan ke nuni da cewar masu kada kuri'ar na cigaba da nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin Merkel ke karbar 'yan gudun hijira a kasar ta Jamus.

A jihar Rhineland-Palatinate da ke yammacin kasar bisa ga dukkan alamu SPD za ta cigaba da mulki inda sakamakon farko ya ba ta kashi 37.5 cikin 100, CDU ta samu 32.5 cikin 100, AfD kashi 11 cikin 100 yayin jam'iyyar kare muhalli ta The Greens ta tsallake da kyar da kashi biyar cikin 100.

Deutschland Landtagswahl Baden-Württemberg Winfried Kretschmann
Firimiyan jihar Baden-Württemberg Winfried KretschmannHoto: Getty Images/T. Niedermueller

A jihar Baden-Württemberg sakamakon farko ya nuna cewa jam'iyyar The Greens da ke jan ragamar mulkin jihar ta samu kashi 32 cikin 100, CDU wadda ta mulki jihar tsawon shekaru 60 zuwa 2011, ta samu kashi 27.5 cikin 100, ita kuma AfD ta samu kashi 13.1 cikin 100, ita kuma SPD da ke cikin kawance a jihar ta samu kashi 13 cikin 100 daga kashi 23 da ta samua 2011.

Masu sharhi dai na ganin irin yadda gwamnatin Angela Merkel ta bude kofofinta ga 'yan gudun hijira na iya zama babban dalilin da ya sanya rashin katabus na jam'iyyarta a zaben a wasu daga cikin jihohin uku.