Zaben majalisar Turai bai yi armashi sosai ba | Siyasa | DW | 25.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben majalisar Turai bai yi armashi sosai ba

Kasa da rabin wadanda suka cancanci kada kuri'a ne suka yi a zabe a kasashe 21 na Kungiyar Gamayyar Turai da zummar zaben wakilai 751 da majalisar Turai ta kunsa.

Tarayyar Jamus da Faransa da Spain da kuma Poland na daga cikin manyan kasashen da aka gudanar da zaben 'yan majalisun Turai a cikinsu a ranar Lahadi. Amma kuma babban kalubalen da suka fuskanta shi ne na rashin tururuwar masu kada kuri'a a runfunan zabe. Alkaluma sun nunar da cewa wadanda suka yi zabe a kashen 21 ba su fi kashi 40% na wadanda suka yi rejista ba.

Sannan kuma a kasar Faransa jam'iyyar FN da ke da ra'ayin rikau ta Marine Lepen ta zargi gwamnati da neman yin murdiya, sakamakon tsaiko da aka fuskanta a lokacin zabe. Alal-hakika dai ba a samu takardun kada wa jam'iyyun Faransa da dama a kan kari a runfunan zabe ba, lamarin da hukumomin Paris suka ce ba zai cire wa zaben armashi ba.

Baya ga bayar da damar zaban 'yan majalisun Turai a wani wa'adin mulki na shekaru biyar, zaben zai kuma bayar da damar zaban sabon shugaban hukumar zartaswa na Kungiyar Gamayyar Turai tsakanin Jean Claude Juncker da kuma martin Schulz.

Wasu kasashen na Turai sun rika sun kammala kada kuri'unsu. Amma kuma da misalin karfe goma agogon Najeriya ne kasar Italiya za ta kammala nata zabe. A daidai wannan lokacin ne za a fara bayar da kwarya-kwaryar sakamakon zabe a daukacin kasashe 28. Amma dai sai ranar litinin mai zuwa ne za a samu cikakken sakamakon zaben na 'yan majalisun Turai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdouhamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin