1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagaye na biyu na zaben Madagaska

Suleiman Babayo MNA
November 19, 2018

An saka 19 ga watan Disamba domin zabe zagaye na biyu a Madagaska tsakanin tsofaffin shugabannin kasar biyu Andry Rajoelina da Marc Ravalomanana.

https://p.dw.com/p/38Y0M
Madagaskar, Antananarivo: Wahlen des Präsidenten
Hoto: picture-alliance/AP/K. Dhanji

Mutumin da yake kan gaba a zaben kasar Madagaska ya yi zargin murdiya kafin fitar da sakamakon karshe domin ganin babu dan takara da ya samu nasara a zaben zagaye na farko.

Tsohon shugaban kasa Andry Rajoelina ya shaida wa dafifin magoya baya a birnin Antananarivo fadar gwamnatin kasar cewa ana duk kokari na hana masa samun fiye da kashi 40 cikin 100 na kuri'u, a zaben da ya wakana ranar 7 ga wannan wata na Nuwamba.

Babu dan takara tsakanin Andry Rajoelina da babban mai dawan da shi wanda shi ma tsohon shugaba kasa ne Marc Ravalomanana. Sakamakon ya nuna Andry Rajoelina yana da kashi 39 da doriya cikin 100, yayin da Marc Ravalomanana yana da kashi 35 da doriya cikin 100. Hukumar zaben kasar ta Madagaska ta ce za a tafi zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ranar 19 ga watan gobe na Disamba.