Zaben Laberiya na kan gaba a jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 29.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Zaben Laberiya na kan gaba a jaridun Jamus

A wannan makon zaben Laberiya da batun dakile kwararar bakin haure daga Afirka da kuma na sakin wani marubuci dan kasar Kamaru ne suka dauki hankulan jaridun Jamus.

Liberia Präsidentschaftswahlen Anhänger George Weah

Al'ummar Laberiya na murnar zaben George Weah a matsayin shugaban kasa

Jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Laberiya ne inda ta ce: Shekaru 12 bayan yunkurinsa na farko na zama shugaban kasa ya ci tura, tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah ya lashe zaben shugaban kasar Laberiya. Dan shekaru 51 ya yi nasara a kan abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai a zaben da aka gudanar zagaye na biyu a ranar 26 ga watan Disamba. Yanzu dai Weah zai gaji shugabar kasa Ellen Johnson Sirleaf mai shekaru 79. Jaridar ta ce al'ummar Laberiya na murna dangane da zaben tsohon dan wasan kwallon kafar George Weah a matsayin sabon shugaban kasa. Weah wanda ya yi alkawarin kawo sauyi a kasar, zai kasance wani mai sulhu da zai dinke tsohuwar baraka da rashin jituwa tsakanin ‘yan Laberiya, kasar da ta yi fama da yakin basasa tsawon shekaru 13 daga 1990 zuwa 2003.

Libyen Flüchtlinge in der Nähe von Tripolis

Matasa da ke kan hanyarsu ta zuwa Turai a wajen da ake tsare da su a kasar Libiya

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon sharhi ta rubuta mai taken Afirka da musabbabin kaura. Ta ce lokacin da matsalar bakin haure ta yi kamari shekaru biyu baya, shugabannin siyasa a Jamus sun nuna sha'awa ga nahiyar Afirka suka ce dole a magance musabbabin yin kaurar ta hanyar inganta halin rayuwa a Afirka. Ban da rikice-rikice da tashe-tashen hankula, rashin hangen makoma ga rayuwa na tilasta matasa daga Afirka tserewa daga kasashensu suna bin hanyoyi masu hadari don zuwa kasashen Turai. An dauki matakai daban-daban bisa manufar magance matsalar. Sai dai a cewar jaridar duk wani mataki da za a dauka ba zai kawo wani sauyi ba, matukar ba bu kyakkyawan shugabanci a kasashen na Afirka. Hasali ma rashin kyawawan yanayi na zuba jari da yawan dogon turanci na tsoratar da ‘yan kasuwa saka jarinsu a Afirka. Jaridar ta ce ana bukatar shugabanci na gari a Afirka, ita kuma nahiyar Turai dole ta tallafa wa gwamnatocin da ke zama abin koyi a nahiyar. Bude kofofin kasuwannin Turai da kawar da shingen cinikaiya don ba wa kasashen Afirka damar kawo hajjojinsu a Turai zai taimaka bisa manufa.


Schriftsteller Patrice Nganang

Shahararren marubuci dan kasar Kamaru Patrice Nganang

Bayan makwanni uku a gidan wakafi, ba zato ba tsammani an sako marubucin nan dan kasar Kamaru Patrice Nganang inji jaridar Die Tageszeitung, inda ta kara da cewa abokan aikinsa a ko ina cikin duniya sun yi ta kamfen na ganin hukumomin Kamaru sun sako marubucin da ke zaman gudun hijira a Amirka. A ranar Laraba wata kotu a birnin Yaoundé ta yi watsi da shari'ar da ake wa Patrice Nganang mai shekaru 47.  A ranar 6 ga watan Disamba aka kamashi lokacin da ya zo fita kasar bayan wata ziyara ta makwanni. Ya dai rubuta wani rahoto a mujallar Jeune Afrique game da yakin da ake yi kan 'yan awaren yammacin Kamaru masu amfani da harshen Ingilishi. Ya yi kira da sauyin gwamnati a Kamaru, kana a shafinsa na Facebook ya yi fata Allah Ya hallaka Shugaba Paul Biya. A saboda haka an zarge shi da yi wa shugaban kasa barazana.