ZABEN KASAR INDONESIA | Siyasa | DW | 07.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZABEN KASAR INDONESIA

default

Ya zuwa yanzu dai Sakamakon zaben da aka samu ya nuna tsahon ministan tsaro Susilo Bambang Yudhoyono na kan gaba da kashi 34 cikin dari na adadin kuriun , yayin da Shugabar kasar mai ci a yanzu Megawati Sukarnoputri take da kashi 27 cikin dari ,Shi kuma Gen.Wiranto. tsohon Jamiín soji a kasar ya sami kashi 22 cikin dari na yawan kuriún kamar yadda bayanai daga hukumar zabe ta kasar Indonesia ya nuna.

To sai dai duk da kasancewa Susilo Bambang ya sami mafi yawan kuriú da kashi 33 cikin dari,amma kuma ya gaza samu yawan adadin da ake bukata.

A yanzu dai batun ko wanene zai yi nasara a zaben ya dogara ne a karawa ta biyu da zaá yi a ranar 20 ga watan satumba.

Idan hakan ta kasance , Megawati zata kara kenan da Gen. Susilo Bamba wanda ya taba rike mukamin ministan tsaro a karkashin gwamnatin ta.

Kimanin mutane miliyan 153 ne suka yi rajistar kada kuria a zaben shugabar kasar ta Indonesia karo na farko a tarihin kasar .

A baya dai yan majalisun dokoki ne suke haduwa su zabi shugaban kasa.

Ko da yake dai zagayen farko na zaben an gudanar da shi lami lafiya , masu lura da alámuran yau da kullum na ganin cewa yanayin siyasar na iya dumama nan da yan makwanni kadan idan zagaye na biyu na zaben ya gabato .

A game da korafi da aka samu a mazabu 2,500 kuwa jamián zabe sun bayyana cewa ana sake kidaya kuriún don tabbatar da wadanda suke ingantattu saboda an sami wasu kuriún an dangwala hannu sau biyu akan su .

A dangane da manufofi, bambanci kadan ne tsakanin yan takarar uku wato Yudhoyono ,Megawati da kuma Witanto.

Ko wane dan takara na fadin cewa zai habaka hanyoyin samun kudin shiga da kyautata tattalin arziki da kuma yaki da ayyukan taáddanci.

Shugabar mai ci a yanzu Megawati Sukarnoputri ta hau shugabancin kasar ta Indonesia ne a shekara ta 2001 bayan da majsar dokokin kasar tayi waje da shi .

Jamaár kasar suna zargin cewa tana sako sako sannan kuma ta kasa ciyar da tattalin arzikin kasar gaba .

Dukkan dai wanda yayi nasarar lashe zaben yana da gagarumin aiki na yaki da yan taádda da kuma magance matsalolin dake dabaibayi ga shaánin cigaban tattalin arziki.

Kasar Indonesia ita ce kasa mafi yawan alúmar musulmi a duniya.

Masu nazarin alámuran yau da kullum na bayyana cewa da zarar an tabbatar da wanda zai kalubalanci Yudhoyono , jamiun zasu shiga zawarcin kananan jamiýu da basu yi nasara ba a zagayen farko don hada karfi wuri guda .