Zaben kasar Chadi | Labarai | DW | 02.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben kasar Chadi

A gobe ne idan Allah ya kai mu, alúmar kasar Chadi za su fita domin kada kuriá a zaben da ake sa ran shugaban kasar Idris Deby zai sake yin tazarce a karo na uku na wasu shekaru biyar a karagar mulki. Sai dai a hannu guda jamaá da dama ba su dauki zaben da wani karsashi ko muhimmanci ba. A bangare guda kuma

hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta baiyana damuwa a game da karuwar hare hare a kusa da sansanonin yan gudun hijira a gabashin Chadi kwana guda bayan da wasu yan bindiga dadi su kimanin 150 suka kashi mutane hudu a wani kauye dake kusa da sansanin yan gudun hijirar. Yan tarzomar wadanda mazauna yankin suka baiyana da cewa ya bangar Janjaweed ne sun yiwa kauyen kawanya inda suka bude wuta a kan mai uwa da wabi.