1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Kamaru na shirin barin baya da kura

Ahmed Salisu MAB
October 9, 2018

Dan takara Maurice Kamto ya yi ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasar Kamaru da ya gudana ranar Lahadi. Gwamnatin kasar ta gargadi al'umma da 'yan siyasa da 'yan jarida da su guji bayyana sakamako ta kowacce siga.

https://p.dw.com/p/36BR2
Kamerun Präsidentschaftswahlen l Maurice Kamto MRC
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Hukumomi a Jamhuriyar ta Kamaru da masu sanya idanu na kungiyar kasashen Afirka ta AU sun ce zaben na ranar Lahadi ya gudana lami lafiya a mafi akasarin kasar, ko da dai an samu 'yan matsaloli nan da can, amma dai ba su yi yawan da za a ce za su iya yin wani mummunan tasiri ga sakamakon zaben da zai fita nan da makonni biyun da ke tafe ba. Ta bangaren tsaro kuwa, hukumar zaben Kamaru din ta ELECAM ta ce ba a fuskanci wani babban kalubale ba kamar yadda Erick Essouse darakta janar na hukumar ya shaidawa DW

Sai dai wani da ya sanya idanu kan zaben kana ya bukaci da a sakaya sunansa ya ce lamarin ba haka ya ke ba. Ya ce "A matsayina na mai sanya idanu na kasance makale cikin wata rumfar zabe na tsawo kimanin sa'o'i 4 saboda harbe-harbe da aka yi ta yi ba kakkautawa. Ban san ko su waye da waye suka yi taho mu gama ba don ina cikin dakin da ake kada kuri'a amma dai mutane da dama ba su samu damar isa rumfar zaben don kada kuri'unsu ba."

Patrice Nganang - kamerunischer Schriftstellers
Marubuci Nganang ya danganta zaben Kamaru da na jeka na yi kaHoto: P. Norman

 Shi ma dai Patrice Nganang da ke zaman malamin jami'a kuma mai sharhi kan harkokin siyasar Kamaru ya nana rashin gamsuwarsa da zaben na jiya inda ya ce "Wannan zaben jeka na yi ka ne domin a jihohi takwas mutane ba su da kwanciyar hankali yayin da a yankuna biyu kuma ake kashe-kashe, abu mai mahimmanci ga irin wadannan wuraren ba shi ne zaben ba, amma yadda za a kawo karshen wannan kisan gilla. Idan muka koma kan zaben kuwa mun san Biya ne zai lashe shi saboda ya yi amfani da karfin soja da kuma dabi'ar nan ta sayen kuri'un zabe."

Wasu al'ummar kasar yanzu haka sun fi karkata hankulansu kan sakamakon zaben da ma irin kwanakin da aka diba kafin a kai ga sakinsa duk kuwa da cewar a wannan zamanin akwai hanyoyi da dama da za a yi amfani da su wajen fidda sakamakon cikin hanzari.