Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Jam'iyyar SPD ta jaddada goyon bayanta ga ministan kudi Olaf Scholz a matsayin dan takaranta na mukamin shugaban gwamnatin Jamus a zaben da zai gudana a watan Satumba mai zuwa.
'Yar majalisa, 'yar kare hakkin jama'a kuma tsohuwar mai wasan motsa jiki: Shugabar jam'iyyar The Greens, Annalena Baerbock ita ce 'yar takarar shugabancin gwamnatin Jamus ta jam'iyyarta.
Za a iya cewa, babu wani yanki a duniya da Merkel ta mayar da hankali a kansa tsawon mulkinta kamar yammacin Afirka. Kama daga jibge sojojin Jamus a Mali da batun bakin haure har zuwa batun tattalin arziki.
Kuri'un jin ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa babu kawancen jam'iyyu biyu da zai yi nasarar samun rinjaye bayan babban zaben ranar 26 ga watan Satumba. Ga takaitaccen bayani.
Tsawon lokaci ya kasance tamkar babu wanda zai gaji shugabar gwamnatin Jamus in ba Armin Laschet ba. Sai dai a yanzu jam'iyyarsa ta CDU ka iya tsintar kanta a bangaren adawa bayan zaben ranar 26 ga watan Satumba.
A duk inda Jamusawa ke zabe, sun fiye son amfani da takardu. Mun shirya muku bayanai a kan hanyoyin da Jamusawa ke bi wajen maganta magudin zabe a lokutansu na zabe.
Har yanzu jam'iyyar hadakar Merkel ta CDU/CSU ba ta tsayar da mai maye gurbinta a zaben kasa na 2021 ba. Amma tuni SPD ta fitar da dan takararta. Kana jami'iyyar kare muhalli ta the Greens, na da 'yan takara biyu.
Yayin da zaben Jamus ke kara karatowa, jam'iyyun siyasa na cigaba da zafafa yakin neman za. Wannan rahoton da muka samar zai yi magana ne kan jam'iyyun Jamus da irin manufofinsu.
Yayin da zaben gama-gari na Tarayyar Jamus ke kara karatowa, wani lamari da ake ci gaba da sanya idanu kan zaben na bana shi ne irin rawar da Jamusawan da ke da tushe daga kasashen waje za su taka a wannan zabe.
An yi hasashen cewar Jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta Angela Merkel CDU na kan gaba a zaben 'yan majalisu na jiha da aka gudanar a Jihar Sachsen Anhalt da ke a kudu maso gabashin Jamus