1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Ya alaka da Amurka bayan zabe?

October 18, 2024

A kokarinta na ci gaba da gogayya da abokiyar hamayyarta a fannin kasuwanci da sauran al'amura na rayuwa, kasar Amurka ta jima da karkakatar da madubin hangenta zuwa ga kasashen da ake kira da Indo-Pacific.

https://p.dw.com/p/4lxGt
Jamus | Berlin | Joe Biden | Frank-Walter Steinmeier
Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa na Jamus Frank-Walter SteinmeierHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Kasashen da ake kira da Indo-Pacific dai, sun kunshi wasua kasashen yankin Asiya da kuma Oceania wato tsibiran da ke dab da Australia. To sai dai babu makawa, alakarta da Jamus na shirin sauya komai cikin kankanin lokaci ba tare da la'akari da ko waye zai lashe zaben shugaban Amurka na watan Nuwamban da ke tafe ba. Shugaban Amurka Joe Biden na ziyara a Jamus, ziyarar da ke zama ta karshe gabanin cikar wa'adin mulkinsa. Babban makasudin ziyarar Biden din ta kwanaki uku shi ne, tattauna halin da Ukraine ke ciki tare da aika wani kakkausan sako ga masu kyamar Yahudawa. Beiden zai kai ziyara cibiyar tunawa da Yahudawan da aka yi wa kisan kare dangi, a yakin duniya na biyu wato Holocaust. Kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da Jamus ta fara yaukaka ne tun bayan yakin duniya na biyun, sakamakon irin tallafin da Washington ta bai wa Berlin domin ta farfado bayan yakin. Peter Sparding shi ne mataimakin shugaban Cibiyar Nazarin Harkokin Mulki da Siyasa da ke birnin Washington, ya ce Amurka ta kashe wa Jamus ta Yamma biliyoyin daloli sakamakon muhimmancin da take da shi a wurinta.

Jamus | Berlin | Joe Biden | Frank-Walter Steinmeier
Kyakkyawar alaka tsakanin Jamus da AmurkaHoto: CHROMORANGE/IMAGO

A shekarar 1961 ne aka gina Katangar Berlin da ta raba kasar zuwa gida biyu, wato Jamus ta Yamma da kuma Jamus ta Gabas. Amurka ta taka gagarumar rawa wajen hade kasashen biyu wuri guda, bayan shekaru 30 ana zaman 'yan marina. Amurka ta jima da karkakatar da madubin hangenta zuwa ga kasashen da ake kira da Indo-Pacific, domin gogayya da Chaina. La'akari da irin masaniyar da ya ke da ita kan rikicin da ya wakana, wannan na daga cikin dalilan da suka sanya Shugaba Biden mara baya ga Ukraine daga mamayar da ta ke fuskanta daga Rasha. Yayin ziyararsa a Jamus din, zai kai rangadi sansanin sojojin saman Amurka da ke Rammstein. Ko ma ya za ta kasance a zaben shugaban Amurkan da za a gudanar kuma ko waye ya samu nasara, masana na da kwarin gwiwar cewa alakar kasashen biyu za ta ci gaba da kara karfafa ganin irin kyakkyawar dangantakar da ta jima tana wakana a tsakaninsu.