1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe ya gudana salin-alin a kasar Mozambik

Binta Aliyu Zurmi MAB
October 15, 2019

Miliyoyin 'yan Mozambik sun gudanar da zaben gama gari na shugaban kasa da na 'yan majalisa da na gwamnoni cikin lafiya da kwanciyar hankali. Ana ganin cewar jam'iyyar Frelimo da ke mulki za ta samu komabaya a zaben.

https://p.dw.com/p/3RLfy
Mosambik Wahl   Manica
Hoto: DW/B. Jequete

Ana ganin cewar matsin tattalin arziki da kasar Mozambik da ke gabashin Afirka ke fuskanta zai iya sa jam'iyyar da ke rike da madafun ikon kasar rasa wasu daga cikin yankunan kasar. An ta fuskantar tashe-tashen hankula gabanin kammala yakin neman zabe a wasu yankuna na kasar da ya yi kaurin suna a fuskar rikicin tawaye.

Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da zaben makamancin wannan a Mozambik tun bayan kulla yarjejeniyar zama lafiya tsakanin Frelimo da ke mulki da Renamo da ta shafe shekaru tana tawaye. A zaben kananan hukumomi da ya gudana a shekarar da ta gabata, jam'iyyar Frelimo da ke mulki ta samu koma baya a wasu yankuna na kasar. Ko a wannan karon ma ana ganin cewar jam'iyyar Renamo za ta iya lashe kujeru a jihohi uku na kasar da ke da arzikin karkashin kasa.