Zabe a jihohi uku a Jamus | Labarai | DW | 26.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a jihohi uku a Jamus

Anan jamus ana gudanar da zabubbuka a yankuna guda uku na kasar,wanda ake kyautata zaton cewa sakamakonsa,zai bayyana irin goyon bayanda gwamnatin hadin gwiwa da Angela Merkel kewa jagoranci ke dashi.Zaben wanda ke gudana a jihohin Baden-Wuerttenberg da Rhineland-Palatinate da Saxony-Anhalt,na masu zama na farkon irinsu tunda Merkel ta haye ragamar mulki a watan Nuwamban daya gabata,a matsayin shugabar jammiyun yan mazan jiya na CDU da CSU,da kuma na social democrates SPD.Wannan zaben na nuni dacewa gwamnatin hadin gwiwan zata cigaba da jagorancin wannan kasa.