Za′a gurfanar da Oscar Pistorius a gaban kotu. | Labarai | DW | 14.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za'a gurfanar da Oscar Pistorius a gaban kotu.

Ana tuhumar ɗan wasan tsereren nakasassu na Afirka ta Ƙudu da laifin kashe budurwarsa a gidansa da ke a birnin Pretoria.

Yan sanda a Afirka ta Ƙudu sun tsare sanannan ɗan wasan tsereren nan Oscar Pistorius, mai ƙafafun roba guda biyu. Wanda shi ne mutun na farko wanda ba shi da ƙafafu da ya halarci gasar wasanin Olympic a shekara bara a Britaniya.

Wani kakakin hukumar yan sanda Katlego Mogale ya ce an kama mtumin ɗan shekaru 26 da haifuwa; sakamako harbe buduwarsa har lahira da ya yi a cikin daran jiya da misalin ƙarfe hudu a gidansa da ke birnin Pretoria.Budurwar mai sunnan Reeva Steenkamp ta mutu nan take saboda raunikan harbin da ta samu.A gobe juma'a za a gurfanar da shi a gaban kotu; sai dai tuni da kakakin yan sandar ya ce an tuhumi Pistorius da laifin aikata kisan kai.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal.