Za´a gana ido da ido tsakanin Bush da Putin a zauren taron G8 | Labarai | DW | 07.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a gana ido da ido tsakanin Bush da Putin a zauren taron G8

An shiga kwana na biyu a taron koli kasashen kungiyar G8 dake gudana a Heiligendamm a nan Jamus, inda ake sa ran yin wata tattaunawa mai zafi tsakanin shugaban Amirka GWB da shugaban Rasha Vladimir Putin. A cikin watannin baya-bayan nan dai Putin ya yi ta saka ayar tambaya game da shirin Amirka na kafa sansanin kakkabo makamai masu linzami a Turai. A nasa bangaren ana sa rai Bush zai nanata zargin da yake yi cewa ana fuskantar tafiyar hawainiya a sauye sauyen demukiradiya a Rasha. Bush ya ce yana farin ciki dangane da tattaunawar da zai yi da Putin.