Za´a ci-gaba da shawarwarin kafa gwamnatin Falasdinawa a Damascus | Labarai | DW | 21.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za´a ci-gaba da shawarwarin kafa gwamnatin Falasdinawa a Damascus

Bisa ga dukkan alamu za´a ci-gaba da tattaunawa tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da jagoran Hamas Khaled Mashaal a birnin Damascus, da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa. Dukkan bangarorin biyu sun ce za´a ci-gaba da shawarwarin bayan kai-komo da jami´an diplomasiyan Syria suka yi. da farko wani babban jami´in Hamas ya ce taron wanda aka dage yin sa a jiya asabar, ba za´a yi shi ba gaba daya. Yanzu haka dai Abbas na birnin Damascus inda ya ganawa da jami´an Syria.