Za je zagaye na biyu a zeɓen Mali | Labarai | DW | 28.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za je zagaye na biyu a zeɓen Mali

Sakamakon wucin gadi na zaɓen 'yan majalisun dokokin da hukumar zaɓen ta bayyana na nuna cewar babu wata daga cikin jam'iyyun siyasar da ta samu rinjaye a zagayen farko.

Hukumar ta ce ya zama dole a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen 'yan majalisun dokokin ranar 15 ga watan Disamba da ke tafe. Daga cikin kujeru 147 da aka ware a majalisar dokokin, kujeru 16 kawai jam'iyyun siyasar da suka yi takara suka samu.

Wadanda suka haɗa da jam'iyyar shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar Keita wato RPM wacce ta sami kujeru guda takwas,da jam'iyyar Soumaila Cisse ta URD da ta samu kujeru biyar yayin da ADEMA ta ke da kujeru guda biyu.Hukumomin ƙasar ta Mali dai sun ce jama'a ba su fito ba a zaɓen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu