Za a yi zaɓen majalisa a cikin watan Nuwamba a ƙasar Holland. | Labarai | DW | 02.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a yi zaɓen majalisa a cikin watan Nuwamba a ƙasar Holland.

Yan gudun hijira daga Africa dake neman shiga Spain

Yan gudun hijira daga Africa dake neman shiga Spain

Ƙasar Holland, ta ba da sanarwar gudanar da zaɓen majalisar dokoki a cikin watan Nuwamba mai zuwa. Hakan dai ya zo ne bayan murabus ɗin da Firamiyan ƙasar, Jan Peter Balkenende ya yi a ran juma’ar da ta wuce, sakamakon saɓanin da ya ɓarke tsakanin jam’iyyarsa da jam’iyyar D66 da ke cikin gwamnatin haɗin gwiwar da yake yi wa jagoranci. A halin yanzu dai Sarauniya Beatrix, ta naɗa tsohon Firamiyan ƙasar, Ruud Lubbers, da ya naɗa sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya har zuwa lokacin zaɓen.