1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a saki fursunonin siyasar kasar Kwango

Abdul-raheem Hassan
March 3, 2019

Shugaba Felix Tshisekedi ya dau wannan matakin ne da zimmar jaddada dorewar dimukuradiyya, tare da yayyafa wa adawar siyasar kasar ruwa a cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa.

https://p.dw.com/p/3ENSE
DR Kongo  Kinshasa Vereidigung Präsident Felix Tshisekedi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Shugaban ya ba da tabbacin 'yanta fursunonin siyasan kasar nan da kwanaki 10, tare da yi musu afuwa. Shugaba Tshisekedi ya ce gwamnatinsa za ta dawo da 'yan kasar da rikicin siyasa ya tilastamusu tserewa zuwa kasashen waje.

A ranar 24 ga watan Janairun 2019 Shugaban Felix Tshisekedi ya sha rantsuwar kama aiki a mtsayin sabon shugaban kasar Kwango, bayan nasarar da ya samu a zaben da ya kawo karshen wa'adin mulkin shekaru Tara da Shugaba Joseph Kabila ya kwashe yana mulki.

Wannan dai shi ne karon farko da jamhuriyar dimikuradiyyar Kwango ta yi nasarar mika mulki cikin ruwan sanyi, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan kasar Beljiyam a shekarar 1996.