1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi sabuwar zanga-zanga a Senegal

March 10, 2021

'Yan adawa a Senegal sun yi kira kan gudanar da sabuwar zanga-zanga a ranar Asabar, kwanaki kadan bayan sakin madugun 'yan adawar kasar da ake zargi da laifin aikata fyade.

https://p.dw.com/p/3qQ5B
Senegal Justiz l Protest von Unterstützern von Sonkoin Dakar
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

A kalla mutane 5 ne suka rasa rayukansu a wata arangama tsakanin 'yan adawan da jami'an tsaro a ranar Laraba saboda kame jagoran 'yan adawan Ousmane Sonko.

Gamayyar kungiyoyin adawa a kasar dai sun bukaci yin zaman makoki a ranar Juma'a tare da bukatar sanya fararen tufafi don nuna alhinin kan wadanda suka mutu.