Za a tuhumi wanda ya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso | Labarai | DW | 16.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a tuhumi wanda ya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso

Janar Gilbert Diendere zai fuskanci tuhume-tuhume masu yawa da suka hada da cin zarafin mutane da kisan kai.

Sojojin da ke gabatar da kara na Burkina Faso sun ce ana tuhumar tsohon wanda ya jagoranci mulki da laifin cin zarafin dan Adam. Janar Gilbert Diendere wanda yake fuskantar tuhuma 10 sun hada da kisan kai. A wannan Jumma'a mai gabatar da kara Kanar Sita Sangare ya ce Diendere zai gurfana a gaban kotun soji, amma bai bayyana lokaci ba.

A watan jiya na Satumba dakarun da ke kare fadar shugaban kasa suka cafke Shugaba gwamnatin wucin gadi Michel Kafando da Firaminista Yacouba Isaac Zida cikin wani juyin mulki da bai samu nasara ba. Tuni mahuktan kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka suka sake saka ranar 29 ga watan gobe na Nowamba domin zaben kasa baki daya.