Za a tsagaita buɗe wuta a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 13.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a tsagaita buɗe wuta a gabashin Ukraine

Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine da takwaransa na Rasha Vladmir Putin sun cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta wacce za ta fara aiki a ranar Lahadi.

Shugabannin ƙasashen Ukraine da Rasha da Faransa da kuma Jamus sun cimma matsaya ɗaya da ke kama hanyar,kawo ƙarshen watannin goma da aka kwashe ana gwabza yaƙi tsakanin dakarun gwamnatin Ukraine da na 'yan aware da ke samun goyon bayan Rasha.

Taron na birnin Minsk wanda a ƙarƙashinsa shugaba Petro Poroshenko na Ukraine da takwaransa na Rasha Vladmir Putin suka cimma yarjejeniyar. Na zaman abin yin hattara a cewar shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande, saboda ko ya ce a ganinsa kafin Lahadin mutane da dama za su iya rasa razukansu

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar