1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a tono gawar Marigayi Arafat domin bincike

November 24, 2012

Hukumar cin gashin kan Palesɗinu ta tabbatar da cewa ranar Talata za a tono gawar Marigayi shugaban Palesɗinawa Yasser Arafat

https://p.dw.com/p/16pGP
Hoto: AP

Hukumar cin gashin kan Palesɗinu ta tabbatar da cewa ranar Talata za a tono gawar Marigayi shugaban Palesɗinawa Yasser Arafat, domin gudanar da bincike ko goba ce ta yi sanadiyar mutuwarsa.

Shugaban kwamitin bincike daga ɓangaren Palesɗinawa Tawfiq Tirawi ya shaida haka ga manema labarai a wannan Asabar. Ya ce bayan ɗaukan kwayoyin halitta domin binciken, za a sake binne marigayi a wannan rana ta Talata.

Cikin watan Nowamba shekara ta 2004 Marigayi Yasser Arafat, ya bar duniya yana da shekaru 75 da haihuwa, a asibitin birnin Paris na ƙasar Faransa. Kuma tun wannan lokaci ake shakku game da mutuwar, saboda ganin yadda rashin lafiyar ya taɓarɓare lokaci guda.

Mawallaf: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh