1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a tallafa wa Afganistan da kudi biliyan 15,6

October 5, 2016

Kasashen duniya a kakashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amirka sun yi alkawarin tallafa wa kasar Afganistan da kudi miliya dubu 13 da miliyan 600 na Euro a cikin shekaru hudu masu zuwa.

https://p.dw.com/p/2Qut5
Afghanistan John Kerry und Salahuddin Rabbani in Kabul
Hoto: Reuters/J. Ernst

Kasashen duniya a kakashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amirka sun yi alkawarin tallafa wa kasar Afganistan da kudi miliya dubu 13 da miliyan 600 na Euro a cikin shekaru hudu masu zuwa domin agazawa shirin sake gina kasar da farfado da tattalin arzikinta . 

Taron kasashen duniya aminnan kasar Afganistan da ya gudana a birnin Brussels ne ya sanar da daukar wannan mataki na tallafawa kasar ta Afganistan. Frederica Mogherini ita ce jagorar majalissar ministocin harakokin waje na Tarayyar Turai: 

"Ta ce mu dukanmu da ke saman wannan tebiri da kamfanonin da kungiyoyi kimanin 100 a shirye muke mu agaza a cikin ko wani taki daya na tafiyar Afganistan. Mun san abin da kamar wuya, kuma tafiya ce mai nisa, amma ba za mu yi kasa a gwiwa ba"

Kasashen duniyar sun sha alwashin talfa wa kasar ta Afganistan wannan kuwa duk da hare-haren da kasar take fuskanta daga mayakan Kungiyar Taliban wadanda ke ci gaba da yin turjiya shekaru 15 bayan kawar da su daga mulkin kasar.