Za a sako Oscar Pistorius daga kurkuku a ranar 20 ga watan Oktoba | Labarai | DW | 15.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sako Oscar Pistorius daga kurkuku a ranar 20 ga watan Oktoba

Da farko an yi watsi da shawarar yi masa afuwa da aka gabatar cikin watan Agusta, yanzu za a kashi wani gida inda zai zauna karkashin wasu ka'idoji.

Rahotanni daga Afirka ta Kudu sun ce a ranar 20 ga watannan na Oktoba za a sako dan tseren kasar rukunin nakasassu Oscar Pistorius da ya taba cin lambobin gasar Olympics sau biyu daga daurin shekaru biyar a kurkuku zuwa daurin talala a gida. Ma'aikatar duba halayyar firsinoni a kasar ta yanke shawarar cewa ana iya sako Oscar Pistorius daga kurkuku a mayar da hukuncinsa zuwa daurin talala. A wannan Alhamis ma'aikatar ta yanke wannan shawara na sakin tsohon dan tseren na rukunin nakasassu, wanda aka same shi da hannu a mutuwar budurwarsa Reeva Steenkamp. Da farko an yi watsi da shawarar farko ta yi masa afuwa a cikin watan Agusta. Ya dai shafe shekara daya daga cikin shekaru biyar na hukuncin da aka yanke masa. Bisa dokar kasar ta Afira ta Kudu dai duk mai laifi da aka yanke masa hukuncin shekaru biyar ko kasa da haka, an iya sakinsa bayan ya yi kashi daya bisa shida.