Za a sake taron ministocin cikin gida na kasashen Turai | Labarai | DW | 15.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sake taron ministocin cikin gida na kasashen Turai

Ministocin cikin gida na kasashen Turai da suka gaza samar da mafita kan raba masu neman mafaka za su sake taro a mako mai zuwa.

Ministocin cikin gida na kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU za su sake gudanar da taron gaggawa ranar 22 ga wannan wata na Satumba, nan da mako guda ke nan, kan bakin da suka kwarara cikin kasashen, bayan gaza samar da wata matsaya yayin taron da aka kammala a birnin Brussels na kasar Beljiyam.

Luxembourg mai rike da shugabancin karba-karba na kungiyar ta ce manufar taron shi ne amincewa da shirin rarraba masu nema mafaka kimanin 120,000 wadanda suke kasashen Girka, da Italiya da kuma Hangari. Lamarin ya ci gaba da janyo rarrabuwan kai tsakanin kasashen na Turai.