Za a karfafa yaki da ′yan ta′ada a yankin Sahel | Labarai | DW | 12.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a karfafa yaki da 'yan ta'ada a yankin Sahel

Chadi za ta jibge dakaru dubu a iyakokin jamhuriyar Nijar da barkina Faso da kuma Mali domin kawo karshen ayyukan masu ikirarin jihadi.

A kokarinta na kawo karshen hare-haren da masu ikirarin jihadi ke kaiwa a yankin Sahel, gwamnatin Chadi za ta kara yawan dakarunta a iyakokin kasashen Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mali.

Kimanin dakarun sojin dubu ne  ake sa ran rarrabawa a iyakokin, bayan da Chadin ta yi tunanin agazawa dakarun Faransa da na Tarayar turai da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Kasar ta Chadi ta ce za ta yi bayanin dalla-dalla yadda rabon zai kasance a wajen taro kan matsalar tsaron yankin da za a gudanar a mako mai zuwa a Birnin N'jamena.

A shekarar da ta gabata dai Faransar ta yi ikirarin samun nasara kan mayakan jihadin da ke tada zaune tsaye a yankin.