Za a gurfanar da wasu ′yan sanda a Baltimore | Labarai | DW | 01.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a gurfanar da wasu 'yan sanda a Baltimore

Ana zargin 'yan sandar ne guda shidda da laifin kashe Freddie Gray wani baƙar fata ɗan shekaru 25 da aifuwa.

Shi dai Freddie Gray ya rasu ne ranar 19 ga watan Aprilun da ya gabata wato Mako ɗaya bayan kamashi a sakamakon raunin da ya ji a wuya lokacin da 'yan sandar suka murɗeshi a ƙoƙarinsu na saka masa ankwa a cikin motarsu.Ko baya ga zargin yin kisan, hukumomin sharia'ar birnin na Baltimore na kuma zargin 'yan sandar da ganawa Fredie Gray ɗin azaba da kuma kamashi ba tare da wani dalili ba.Mutuwar wanann baƙar fata dai na daga cikinn dalillan da suka haddasa zanga-zanga da ƙone-ƙone a birnin na Baltimore da ma wasu garuruwan ƙasar ta Amrika a tsakiyar wannan mako.