Za a gudanar da zaben Kanada a watan Oktoba | Labarai | DW | 02.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a gudanar da zaben Kanada a watan Oktoba

Firaminista Stephen Harper na Kanada zai kira zabe majalisar dokoki domin gudanarwa ranar 19 ga watan Oktoba mai zuwa

Wani lokaci a wannan Lahadi ake sa ran Firaminista Stephen Harper na kasar Kanada zai kira zabe majalisar dokoki domin gudanarwa ranar 19 ga watan Oktoba mai zuwa. Hanyoyin bunkasa tattalin artikin kasar za su mamaye yakin neman zaben na makonni 11.

Ofishin firaministan ya ce idan an jima da rana Harper zai ziyararci shugaban jeka na-yi-ka David Johnston wanda yake wakiltan Sarauniyar Elizabeth ta Ingila, domin shaida masa ranar zaben.

Firaminista Stephen Harper dan shekaru 56 da haihuwa, ya dare madafun ikon tun shekara ta 2006, inda ya shafe shekaru 10 yana mulkin kasar ta Kanada karkashin jam'iyyar mai ra'ayin zaman jiya.