Za a gabatar da wani shirin sulhu a Yaman | Labarai | DW | 31.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a gabatar da wani shirin sulhu a Yaman

Wakilin musammun na MDD a Yaman Ismail Ould Cheik Ahmed ya ce zai sake komawa ga shirya shirin suhu tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a kasar.

Shirin sulhun dai na farko ya tanadi janyewar 'yan tawayen Houthis 'yan Shi'a daga yankunan da suka mamamaye tun a shekara ta 2014, tare kuma da dakatar da bude wuta.Cheik Ahmed ya  bayyana wa kwamitin sulhu na MDD cewar zai tattauna  da dukkanin sassan biyu domin cimma wata yarjejejiniya da za ta samu amincewa tsakanin bangarorin.