Za a duba batun bai wa Britaniya karin lokaci | Labarai | DW | 15.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a duba batun bai wa Britaniya karin lokaci

'Yar takarar shugabancin Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce idan har ta yi nasarar zama shugabar hukumar, za ta goyi bayan bai wa kasar Britaniya karin lokaci na ficewa daga kungiyar.

'Yar takarar shugabancin Hukumar Tarayyar Turai kana ministar tsaron kasar Jamus Ursula von der Leyen ta ce za ta goyi bayan ba wa kasar Birtaniya karin lokaci idan har akwai bukatar yin hakan, matukar ta sami nasarar zama shugabar hukumar. Von der Leyen ta bayyana hakan ne cikin wata wasika da ta mika ga 'yan majalisar jam'iyyar Socialist da 'yan Liberal.

A ranar Talata 'yan majalisar Tarayyar Turan za su kada kuri'unsu a asirce domin zaben sabon shugaban Hukumar ta Tarayyar Turai. Sai dai akwai fargaba daga wasu bangarorin da ke tunanin ba za ta kai labari ba, wanda tuni jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli suka ce ba za su zabe ta ba.