1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Za a biya Sadat Ilya Dan Malam diyya

Gazali Abdou Tasawa
June 25, 2021

Kotun ECOWAS ta umurci gwamnatin jamhuriyar Nijar da ta biya diya ta miliyan 50 na CFA ga dan fafutika Sadat Ilya Dan Malam na Kungiyar MPCR bisa daure shi ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/3vYz2
Symbolbild | ECOWAS | Westafrikanischer Regionalblock verabschiedet neuen Plan zur Einführung einer einheitlichen Währung im Jahr 2027
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Kotun ECOWAS ta umurci gwamnatin Nijar da ta biya diya ta miliyan 50 na CFA ga dan fafutika Sadat Ilya Dan Malam na Kungiyar MPCR, wanda aka tsare har na tsawon watanni 18 ba bisa ka’ida ba a gidan kurkuku. 

Dan fafutukar ya shiga hannun ne, bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnati, bayan da ya shirya wata zanga-zanga a jihar Damagaram. Kotun ta kuma ce matakin da kasashen G5 Sahel suke dauka na haramta zanga-zangar lumana a bisa hujjar yaki da ta'addanci ko tabbatar da tsaro ya saba wa dokokin kasa da kasa.