Zaɓen shugaban ƙasar Jamus | Labarai | DW | 30.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasar Jamus

A yayinda 'yan majalisar Tarayyar Jamus suka fara zaben sabon shugaban kasa, an kammala zagayen farko amma babu wanda ya samu rinjaye.

default

Babban Taron Tarayyar Jamus a bara

A yau ne majalisar tarrayar Jamus take saɓen sabon shugaban kasa. Shugaban ƙasar wanda marar cikakken iko ne, wakilai a majalisar dokoki ta Bundestag, da kuma wakilai daga majalisun jihohine za su haɗu don zaɓar shugaban ƙasar a yau. Haɗin gwiwar jam'iyun da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke jagoranta, suna da kujeru 644 daga cikin kujeru 1244 na majalisar, don haka ake saran ɗan takaransu Christian Wulff zai iya samun nasara. To sai dai shi ma ɗan takaran jam'iyar Social Demokrat, Joachim Gauck yana samun ƙarin karɓuwa na mamaki. Izuwa yanzu dai an yi zaben tsagayen farko babu wanda ya samu rinjaye, don haka aka koma zagaye na biyu. Zaɓen ya biyo bayan murabus ɗin tsohon shugaban ƙasar Horst koehler ya yi, biyo bayan sukar da aka yiwa kalamansa, na cewa kasancewar sojin Jamus a Afganistan, yana nasaba da batun tattalin arziki.

MAwallafi: Usman Shehu Usman       

Edita: Umaru Aliyu