Zaɓen shugaban ƙasa a Tsibirin Sao Tome da Principe | Labarai | DW | 30.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Tsibirin Sao Tome da Principe

A cen ma tsibirin Sao Tome da Principe, yau ne al´ummar ƙasar ke zaɓen shugaban ƙasa.

Baki ɗaya yan takara 3, su ka shiga gwargwamayar haye wannan kujera mai daraja.

Yan takara, sun haɗa da shugaba mai barin gado,Fradique de Menes, da aka zaɓa a shekara ta 2001.

Akwai kuma Patrice Trovoada, ɗan tsofan shugaban ƙasa Miguel Trovada, da ya mulki Sao Tome da Principe, daga shekara ta1991 zuwa 2001.

Ɗan takara na 3, wani hamshaƙen ɗan kasuwa ne, Nilo Guimares.

Kamar yada kudintsarin mulkin tsibirinya tanada idan babu wanada ya lashe zaben tun zagaye na fako za ashirya zagaye na 2 cikinkwanaki 15 masu zuwa.

An kamalla yaƙin neman zaɓe ranar juma´a cikin kwanciyar hankali.

Babban aikin da ke jiran shugaban da zai nasara lashe wannan zaɓe, shine na na haɓaka tattalin arzikin wannan tsibiri, mai arzikin man petur, wanda kuma yawan mutanen sa, su ka kai, dubu 140.