Zaɓen shugaban ƙasa a Poland | Siyasa | DW | 20.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen shugaban ƙasa a Poland

Yan ƙasar Poland miliyan 30 ne suka fita kaɗa ƙuri'a a zaɓen da ake fatan samun wanda ya zai gaji marigayi tsohon shugaban kasar

default

Ɗan takara Jaroslaw Kaczynski ɗan uwan marigayi tsohon shugaban ƙasar Poland.

Al'umar ƙasar Poland sun fita kaɗa ƙuri'a domin zaɓar wanda zai maye gurbin tsohon shugaban ƙasar Lech Kaczynski wanda ya rasu a haɗarin jirgin sama a Rasha a ranar 6 ga watan Aprilu. Mutane kimanin Miliyan 30 ne ake sa ran za su fita domin kaɗa ƙuri'arsu.

Har yanzu dai al'umar ƙasar ta Poland suna cikin alhini na bala'in haɗarin jirgin saman da ya auku. Wannan ya jefa ɗaukacin al'umar ƙasar cikin ruɗani. Hasali ma dai a cewar shugaban sashen Jamusanci na tashar gidan Radion Poland Joachim Ciecierski hakan ya shafi yanayin yaƙin neman zaɓe wanda ya kasance babu karsashi ba kamar yadda yan siyasa suka saba yaƙin neman zaɓe ba.

" Yan siyasar dai na amfani ne da wasu kalamai na daban, babu karsashi mai ƙarfi ga yaƙin neman zaɓen kamar yadda aka saba yi a Poland. Yan takarar dai kan yi tunani mai zurfi kafin su furta dukkan wasu kalaman da suke so su faɗa. Ba shaguɓe ba cin zarafi, yanayin dai ya kasance shiru, ko da yake ana iya jin ɗari ɗari da motsa zukata kasancewar wannan muhimmin zaɓe ne na ƙasa baki ɗaya".

Haɗarin jirgin dai bama kawai ya sauya hayaniyar zaɓen bane kaɗai, har ma da lisafi da yanayin tsarin siyasar baki ɗaya. Kafin aukuwar haɗarin dai farin jinin shugaban ƙasar kuma shugaban Jam'iyar yan mazan jiya Lech Kaczynski ya yi ƙasa kamar yadda alƙaluman ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a suka nuna. Kusan ma dai jama'a sun yi amanna cewa zai yi matuƙar wuya ya iya sake cin zaɓe a karo na biyu, sai dai kuma yanayin da rasuwar tasa ta zo ya yi gagarumin sauyi da ɗaukaka ƙima da martabarsa a idanun al'umar ƙasar. Wannan shine abin da ɗan uwan tagwaitakarsa da kuma shugabannin adawa suke hakoron ɗamfarewa akansa.

Tare da alƙawarin cewa zai ƙarasa ayyukan da marigayi ɗan uwansa ya faro, ya amince da shiga takara, a yan makonnin da suka gabata ya ƙudiri wannan aniya gadangadan. Ita ma Jam'iyar ta yan kishin ƙasa masu ra'ayin mazan jiya ta amince da buƙatar da jama'a suka nuna ta goyon Jaroslaw Kaczynski ɗan uwan marigayi shugaban ƙasar ta Poland Leck Kaczynski.

A yanzu dai tazarar da ada take tsakanin ɗan takarar adawa na Jam'iyar Liberal Civic Platform Bronislaw Komorowski da kuma Jaroslaw Kaczynski ta ragu daga kashi 20 cikin ɗari zuwa kashi bakwai cikin ɗari. A cewar Joachim Ciecierski ɗan jarida a birnin Warsaw an buɗe sabon daga tsakanin yan takarar biyu.

Präsidentschaftswahl in Polen 2010 Jaroslaw Kaczynski

Jaroslaw Kaczynski na jam'iyar mazan jiya.

" A baiyane yake daga ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a cewa mutane da dama za su jefa ƙuri'arsu ce ga Jaroslaw Kaczynski, basa tare da jam'iya adawa, za kuma su yi haka ne ba don kamai ba sai saboda kasancewarsa dan uwa ga marigayi Leck Kaczynski".

A yanzu dai ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna Komorowski na da kashi 42 cikin ɗari yayin da Kaczynski ke da kashi 36. Wannan shine hasashe sakamakon zaɓen. Sai dai kuma idan jama'a da dama basu fito ba, hakan ka iya taimakawa Kaczynski. Abin jira dai a gani shine yadda zaɓen zai kaya.

" Za mu gani dai ko wanene zai yi nasara, amma dai abin da yake tabbas shine cewa za'a je ga zagaye na biyu, ba za'a sami wanda zai nasara kai tsaye a zagayen farko ba".

Cikin makonni biyu dai za'a gudanar da za'a gudamnar da zaɓen zagaye na biyu, idan kuma akai ga wannan matsayi, to babu tabbas ko Jaroslaw Kaczynski zai iya yin galaba akan yan adawa. Sai dai damar da yake da ita, ita ce sake yin shiri da ɗaura ɗamara a zaɓe na gaba na shekarar 2012.

Mawallafa :  Bartosz Dudek/Abdullahi Tanko Bala

Edita : Mohammed Nasiru Awal