Zaɓen raba-gardama a Masar | Labarai | DW | 02.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen raba-gardama a Masar

Nan da makonni biyu ne Misirawa za su jefa ƙuri'ar yin na'am da daftarin tsarin mulkin ƙasar ko kuma watsi da shi.

Shugaba Mohammed Morsi na ƙasar Masar ya bayyana cewar a ranar Asabar 15 ga watan Disamban nan ne, al'ummar ƙasar za ta jefa ƙuri'ar raba gardama a kan sabon daftarin tsarin mulkin ƙasar. Wannan sanarwar ta zo ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar bisa ƙarfin ikon da shugaba Morsi ya ƙara wa kansa a makon da ya gabata, wanda ya hana kotuna hurumin ƙalubalantar shawarwarin da zai zartar.

Morsi ya bayyana cewar hakan wani mataki ne na wucin gadi a koƙarin hanzarta mayar da Masar a karƙashin turbar Dimokraɗiyya gabannin samar da sabon tsarin mulki. Shugaba Mohammed Morsi ya sanar da ranar gudanar da zaɓen raba gardamar ce yayin wani shagalin karɓar kofi na daftarin sabon tsarin mulkin a wannan Asabar daga majalisar rubuta tsarin mulkin da wakilan jam'iyyarsa ta 'yan uwa Musulmi suka fi rinjaye, wadda kuma ta yi gaggawar amincewa da tsarin mulkin yini daya gabannin hakan. Wakilin DW ya ruwaito cewar Misirawa suna da mabanbantan ra'ayi game da ƙuri'ar raba gardamar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal

 • Kwanan wata 02.12.2012
 • Rahotanni masu dangantaka Masar
 • Muhimman kalmomi Masar
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16uLB
 • Kwanan wata 02.12.2012
 • Rahotanni masu dangantaka Masar
 • Muhimman kalmomi Masar
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16uLB