Zaɓen Lahadi: Steinbrück ko Merkel? | Jigo | DW | 04.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Jigo

Zaɓen Lahadi: Steinbrück ko Merkel?

Ko da yake komai ka iya faruwa a maraicen 22 ga watan Satumba, amma dai akwai kyakyawan alamun cewar Angela Merkel ce za ta iya samun nasara.

To amma kawo yanzu Peer Steinbrück ɗan Social Demokrat na ta yin gwagwarmaya bakin rai bakin fama. Ba shakka ƙalubalen mai wahala ne kuma ɗan takarar shi ne mafi cancanta a lokacin da ya kamata. Peer Steinbrück ƙwarrare ne a kan sha'anin kuɗi sannan ya riƙe matsayin ministan kudi a cikin gwamnatin Angela Merkel ta ƙawance jam'iyyun siyasa na CDU da CSU da kuma SPD a lokacin da matsalar ta kuɗi ta kuno kai wacce ta shafi tattalin arzikin ƙasashen Turai da dama don haka ya na da masaniya so sai a kan sha'anin kuɗi da tsarin kasafin na ƙasar ta Jamus ga kuma abin da ya bayyana a lokacin da yake magana a lokacin wani gangamin siyasa. Ya ce: '' Ina son na zaman shugaban gwamnatin Jamus.''

Goggaya tsakanin 'yan takara biyu za ta kasance mai tsauri

Angela Merkel ta zama shugabar gwamnati a shekara 2005

Angela Merkel ta zama shugabar gwamnati a shekara 2005

Goggayar za ta kasance mai wuya ga Steinbrück wanda tun kafin a je ko'ina ake ganin da ker zai iya yin wani hoɓasa a gaban yar takarar ta jam'iyyar CDU wato Angela Merkel, wacce jam'iyyarta ke daf tsakiya cikin maganar ƙara darajar takardar kuɗin Euro da kuma nazarin irin basusukan da suka dabaibaye ƙasashen nahiyar ta Turai, Merkel mace ce, da ta nuna bajinta a fagen siyasa na tsarin tafiyar da al'amuran na ƙungiyar Tarrayar Turai kuma yawancin Jamusawa na girmamata kuma suna begenta.

Sai dai wannan ba ya hanna abokan addawa na jam'iyyar SPD yin suka ga shugabar gwamnati to amma Christophe Moss wani kwarrare a kan al'amuran sadarwa ya ce sukar ba za ta iya sauya komai ba. Ya ce: '' Koma jam'iyyar ta SPD ta faɗi wani abu marasa daɗi ko kyau a kan 'yar takarar, duk da haka Jamusawa sun gamsu da aikinta.''

Manufofin zaɓe na 'yan takarar guda biyu

Designated top candidate of the German Social Democratic Party (SPD) for the 2013 German general elections, Peer Steinbrueck delivers his speech during the extraordinary party meeting of the SPD in Hanover, December 9, 2012. More than 500 delegates are supposed to elect Peer Steinbrueck as the SPD's top candidate for Germany's 2013 general elections. REUTERS/Kai Pfaffenbach (GERMANY - Tags: POLITICS)

Peer Steinbrück dan takarar SPD

A fagen da za a bambanta 'yan duma da 'yan kabewa a zaɓen tsakanin 'yan takarar biyu shi ne a kan manufofin siyasa na program na kowane ɗan takarar. SPD a tsarin manufofinta tana buƙatar da a tsaida albashi mafi ƙankanta a awa ɗaya a Jamus a Euro takwas da rabi ,to amma ƙawance jam'iyyun siyasar CDU da CSU na addawa da shi domin suka ce haki ne da ya rataya a kan ƙungiyoyi ma'aikata da sauransu wajen tsaida albashin.

A tsarin haraji SPD na neman kaso mai tsoka na haraji daga attajirai yayin da ƙawance da ke goyon bayan Merkel ke son rage basusukan da ke a kan gwamati tare da rage yawan kuɗaɗen haraji kuma Merkel ta kare manufofinta na siyasa.Ta ce: ''manufofi ne na haƙida ta masu matsagaicin ƙarfi da ke sauke ƙarin nauyi a kan al'umma da kuma tattalin arzikin ƙasar''.

Mawallafi : Volker Wagener / Abdourahamane Hassane
Edita: Umaru Aliyu

DW.COM

Karin shafuna a WWW

Sauti da bidiyo akan labarin