Zaɓen jihohi a Faransa | Siyasa | DW | 15.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen jihohi a Faransa

Jam´iyar UMP ta Nicolas Sarkozy ta sha kashi a zagayen farko na zaɓen jihohin ƙasar Faransa

default

Nicolas Sarkozy ya sha kashi a zaɓen jihohin Faransa

Shugaban ƙasar Faransa Nikolas Sarkozy ya ci rabin wa´adin mulkinsa,to saidai  ya sami kansa cikin wani mummunan yanayi na dushewar tarmamuwarsa.Zagayen farko na zaɓen jihohi da aka shirya jiya  a faɗin Faransa ya nuna shaida ƙarara, inda jam´iyarsa ta UMP da abokan ƙawancenta suka sha mummunan kayi.

Wani karin maganar hausa ke cewa  "na san a rina", duk ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a da cibiyoyin hasashe suka gudanar, sun gano cewar jam´iyar UMP ta shugaba Nikolas Sarkozy ba zata taka rawar azo a gani ba a zagayen farko na wannan zaɓe, ta la´akari da rashin gamsuwar da mafi yawan faransawa ke nunawa, ga kamun ludayin mulkin shugaba Nicolas Sarkozy.

Jam´iyar PS ta Martine Aubry tare da sauran jam´iyu masu ra´yin gurguzu sun wa UMP da abokan ƙawancenta fintikau, a zagayen farko na wannan zaɓe, to saidai har yanzu da sauran rina kaba inji Martin  Aubry:

" Ba a fita daga ruwa ba, ba a matse wando, komi na iya faruwa duk da cewar mun sami nasara a zagayen farko.Akwai sauran aiki sati mai zuwa a zagaye na biyu, saboda haka ina kira ga faransawa masu goyan bayanmu, su ƙara zage damtse don mu tabbatar da wannan rinjaye da muka samu."

Da yake jawabi game da sakamakon wannan zaɓe Firaministan ƙasar Faransa Franßois Fillon,yace ko kusa ba su da fargaba suna da cike da burin lashe zagaye na biyu da aza a shirya ranar lahadi mai zuwa:

"Rashin halartar mutane da himma  a runfunan zaɓe ba zai bada damar a ɗauki wani darasi daga zaɓen ba.Saɓanin ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a da aka yi tayi kamin zaɓe, wanda kuma ke nuni da cewar UMP zata sha mummunan kayi,har yanzu ba a san ma ci tuwo ba, sai kiya ta ƙare".

Banda jam´iyar PS sauran jam´iyu masu raá yin gurguzu da suka kawo kalo a zaɓen na jiya sun haɗa da jam´iyar FN mai tsatsauran ra´ayin wariya,ta Jean Marie Lepen, da kuma jam´iyar ´yan radin kare mahhali ta Daniel Cohn Bendit, wanada yayi kira ga dukkan jam´yun  masu aƙidar gurguzu su hada kai:

"Yauni ya rataya akan dukkan masu adawa wanda ke da aƙidar gurguzu kamo daga magoya bayan PS da masu radin kare mahalli da makamantansu, su zama tsinstiya maɗaurinki ɗaya a zagaye na biyu, domin cimma gagaramar nasara, wannan shine babban darasin da za aiya dauka daga zagayen farko na zaɓen."

A halin da ake ciki dai tunni ɓangarorin biyu sun shiga yaƙin neman zaɓen zagaye na biyu da za a shirya ranar lahadi mai zuwa.Sakatare Janar na jam´iyar UMP mai mulki Xavier Bertrand a jawabin da yayi yau, yayi kira ga dukkan wanda ba su yi zaɓe jiya ba, su hitto da himma a zagaye na biyu.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Halima Balarabe Abbas